Uncategorized

labari da dumi duminsa:Yan bindiga sun sace malai da daliban makaranta a Lagas

An rahoto cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai hari wani makarantar sakandare a jihar Lagas
– An ce yan bindigan sun sace dalibai da jami’an makarantar
– Biyu daga cikin daliban sun samu yancin su

Wasu yan bidiga sun sace Dlibai da malaman makaranta
Akwai tsoro a cikin birnin Lagas, bayan wani hari da aka kai a makarantar sakandare, daga wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba.
Yan bindigan da ba’a sani ba har yanzu, sun sace dalibai da malaman makarantar gwamnatin Igbonla, Epe a ranar Alhamis 6 ga watan Oktoba.
Bayan afkuwar wannan mummunan al’amarin, majalisar wakilai sunyi kira ga hukumomin tsaro a kasar da su tabbatar sunyi kokarin ceto malaman makarantar da daliban da aka sace.
Kiran yazo nan da nan bayan yan sanda sun tabbatar wa manema labarai cewa an saki biyu daga cikin daliban yayinda ake ci gaba da neman sauran, wanda suka hada da shugaban makarantar.
Yan majalisan sunji daga bakin Mr Raji yanda wasu masu satar mutane suka kai hari ga makarantar gwamnati Igbonla, Epe a safiyar ranar Alhamis, lokacin da daliban ke addu’an safe na shiga makaranta.
Kakakin yan sandan jihar Lagas, Bisi Kolawole, ta fada ma manema labarai cewa an ceto biyu daga cikin daliban, wanda ya rage dalibai guda biyu, malama daya da kuma shugaban makaranatar.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button