Sports

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya fadi lokacin da zai yi ritaya



Fitaccen dan wasan duniya, Cristiano Ronaldo yace ya kusa ritaya ya ajiye kwallo
– Dan wasa Ronaldo ya bugawa Man Utd da Real Madrid wasanni kusan 645
– Dan wasan ma shekaru 31 a duniya yace girma ya fara kama DA

Dan wasa Cristiano Ronaldo na Real Madrid yace ba za a dade ba zai ajiye wasan kwallon kafa domin girma ya fara kama sa. Dan wasan gaban na Real Madrid ya zura kwallaye a Kungiyar fiye da 360 cikin wasanni kusan 350 da ya buga mata.
Dan wasan duniya Ronaldo mai shekara 31 da haihuwa yace shekarun sa sun fara tafiya don haka zai ajiye kwallo nan da wani lokaci ba mai yawa ba. Dan wasa Ronaldo yace shekarun da suka rage masa na taka leda ba za su kai goma ba. Ronaldo yace sai ya fara haring aba kuma.
Cristiano Ronaldo yace ba zai dawwama yana buga kwallon kafa ba a rayuwar sa, don haka dole ya fara neman wani abin yi duk yadda yake sha’awar kwallon kafar kuwa. Duk da dai cewa dan wasan ya zarce shekaru talatin, amma har yanzu bazar sa tana rawa. Cristiano Ronaldo ya sha zuwa na daya a duk duniya.
Dan wasa Cristiano Ronaldo ya bugawa Kungiyar Sporting ta gida da kuma Man Utd ta Ingila, sannan Real Madrid da yake yanzu. Ronaldo yaci kwallaye fiye da 500 a gida da kuma kulob. Yanzu haka shine Kyaftin din Kasar Portugal.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button