Uncategorized

Arangamar jami’an tsaro da yan shi’a tayi sanadiyar mutuwar mutane 10, mutanen garin na murnar (Hotuna)

Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya na cewa an kashe akalla mutum 10 lokacin da ‘yan kungiyar ‘yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi’a suke taro.
Shia
Bayanan da majiyar mu ta samu sun ce lamarin ya faru ne a garin Funtua lokacin da ‘yan sanda da sojoji suka yi yunkurin hana ‘yan Shi’a yin tattaki da suka saba yi duk shekara domin tunawa da ranar Ashura.
Wani ganau ya shaida wa majiyar tamu cewa ya kirga gawarwakin mutum takwas.
Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.
Ya kara da cewa an jibge jami’an tsaro a kusa da wurin da suke yin tattakin domin hana su, yana mai cewa jami’an tsaron sun rika harba bindiga sama domin tsorata jama’a.
KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Sojoji sunyi arangama da yan shi’a a Kaduna
Da ma dai jihohin Kaduna da Kano da kuma Katsina sun hana ‘yan Shi’a yin tattaki a wannan shekarar.
Hasalima, jihar Kaduna ta haramta kungiyar saboda zarginta da keta dokoki da kuma tayar da zaune tsaye, zargin da suka musanta.
Sai dai kuma wata majiyar tamu ta ruwaito cewa A dai-dai wannan lokaci, a cikin Garin Funtua dai kura ta Fara lafawa inda Jami’an tsaro bisa taimakon Matasa suka ci Galabar mabiya akidar ta Shi’a.
Yanzu da kura ta lafa, Jami’an tsaro sunyi nasarar Kama wasu daga cikin Mabiya akidar ta Shi’a musamman Mata, da kuma Raunata Mabiya akidar ta Shi’a. A Cewar wasu kusan An kashe ‘yan Shi’an ba mutum daya ko biyu ba.
A bangaren al’ummar garin kuwa, sun nuna farin cikinsu inda suke cewa “Wani Buratai Ya Sauka a Garin Funtua’, sannan da tafawa Jami’an tsaron na Sojoji da Yan sanda.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button