Sports

Zage Damtse Shine Gaskiya Manchester United

Danwasan Manchester United Juan Mata yayi kira ga takwarorinsa ‘yan wasan Manchester United da su dage su zage damtse wajan ganin sunyi kukari samun nasara a wasanninsu na gaba.
Mata ya nuna rashin jin dadin ganin yanda Kungiyar tayi wasanni har guda 3 ajere ba tare da samun nasara ba, Inda Manchester City ta bita har gida ta shata 2-1, a gasar firimiya na bana.
Hakanan kuma Feyenoord na kasar Netherland ta shata 1-0 a gasar Lig din nahiyar Turai, na bana, Itama Watford ta lallasa Manchester United 3-1 a wasannin firimiya, Juan Mata ya ce wannan shine karo na farko da aka doke Jose Mourinho a wasanni uku ajere tun shekara ta 2001-02 lokacin ya na Kungiyar UDL dake Portugal.
Gobe ne in Allah ya kaimun Manchester United, zata kara da Northampton Town a gasar :Lig na kasar Ingila, na bana zata kuma kara da Leicester City a wasannin firimiya, mako na 6.
Dan kasar Spain kuma dan wasan Manchester United, Juan Mata ya ce inda har suka samu nasara a wasanni biyu da Manchester united, zatayi zai kara farfado da martaban kulob din a idon magoya bayanta a fadin duniya.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button