Uncategorized

Taurin kan Buhari ne ya jefa talakawa cikin mawuyacin hali inji Bafarawa

Bafarawa ya ce babu abunda ya janyo haka illa rashin karba ko yin shawarwari da wadanda suka dace
Bafarawa ya kara da cewa yayin da ‘yan Nijeriya suke fadin albarkacin bakinsu kan tsananin rayuwa, shi a nasa ra’ayin, babu mai laifi sai shugaban kasa domin tilas ne ya zamanto mai karbar shawara.
Yace ya rubutawa shugaba Buhari wasiku domin neman ya gan shi ya ba shi shawara, amma har yanzu bai sami amsa ba.
Bafarawa yace wannan musiba da aka shiga ta shafi kowa, ba tare da la’akari da jam’iyya ba.
Saboda haka idan za’a shawo kanta, dole shugaba ya saurari kowa.
Bafarawa wanda jigo ne a jam’iyyar ‘yan hamayya watauPDP, ya zargi ‘yan arewa da tsuke bakunansu kan matsalolin da gwamnatin Buhari take fuskanta.
Yace idan shugaban yana jin ba’a zaginsa da gwamnatinsa, to zaisha mamaki, domin ana yi,don tsoro yasa ba’a gaya masa.
A martanin da ya bayar kakakin fadar shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya kwatanta maganar Bafarawa, da ‘yan fashi da za su shiga gida cikin dare su wawushe komi, sannansu komo da rana suna tambayar mai gidan cewa yayaaka yi ba shi da abinci a gidan.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button