Uncategorized

SOKOTO, ZAMFARA DA BAUCHI SUNE KAN GABA WAJEN SATAR JARABAWAR NECO

SOKOTO, ZAMFARA DA BAUCHI SUNE KAN GABA WAJEN SATAR JARABAWAR NECO
Hukumar kula da jarabawar karshe ta makarantun sakandare wato NECO ta bayyana a ranar Juma’a, cewa sakamakon jarabawar da aka gudanar a watannin Yuni/Yuli na shekarar 2016 ya fita.
Da yake bayyanawa magatakardar Hukumar jarabawar Professor Charles Uwakwe, Ya tabbatarda cewa dalibbai 1, 027, 016 ne sukayi rigistar jarabawar yayinda dalibbai 1, 022, 474 ne suka samu damar zauna jarabawar darussa 76, Wanda kuma 905, 011, suka samu nasarar cin darussa 5 tare da Darasin Lissafi da turanci (Wanda kashi 88.51% ne suka samu).
Charles, ya bayyana dalibai da makarantu daga jihohin Sokoto, Zamfara da Bauchi sune gaba gaba wajen satar jarabawar NECO yayin da babban birnin tarayya Abuja, Bayelsa da Ekiti sune wadanda keda karancin kurafe korafen satar jarabawa.
Sources:
Sakkwato Birnin Shehu
18th September, 2016
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button