Uncategorized

Rikicin APC: Tinubu ya nemi Oyegun ya yi murabus

Rikici ya barke a jam’iyyar APC mai mulkin Nigeria bayan da tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa da ya yi murabus.

Mista Tinubu ya zargi John Odigie-Oyegun da yi wa “demokuradiyya zagon kasa” sakamakon rawar da ya taka a zaben fitar da gwani na jam’iyyar a jihar Ondo.
A wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Lahadi, jagoran na jam’iyyar APC ya ce Mista Oyegun ya karya ka’idojin demokuradiyya da aka shimfida jam’iyyar a kai.
Ya ce an kafa APC ne a kan turbar adalci da demokuradiyya, sai dai ya ce wadannan abubuwa na fuskantar barazana daga wadanda ba su da asali a jam’iyyar.
Sakamakon zaben na jihar Ondo, wanda Rotimi Akeredolu ya lashe, ya bar baya da kura, domin dan takarar da Tinubu ya ke goyon baya, Segun Abraham, ya yi watsi da shi.
Kawo yanzu dai Mista Oyegun ko kuma shugabancin jam’iyyar ta APC ba su ce komai game da wannan batu ba.
Martanin Shugaba Buhari
Sanarwar ta Mista Tinubu ta ce wadanda suka kafa jam’iyyar sun fahimci cewa adalci ne zai sa ta karbu sannan jama’a su aminta da tsarin cigaban da aka kafa ta a kai.
A cewarsa: “Idan jam’iyyar ba za ta yi adalci a kan kanta ba, to zai yi wuya ta samar tare da kafa gwamnati mai adalci
a fadin kasar“.
Mista Tinubu ya ce a baya jam’iyyar ta zama abar misali na adalci da shimfida tafarkin demokuradiyya tsakanin ‘ya’yanta da kuma ‘yan kasar baki daya.
Amma, a cewarsa, “a yanzu wadancan alkawura abubuwa ne kawai da ake fada a baki wadanda babu su a aikace, kuma Oyegun ya yi watsi da wadannan turaku da aka kafa jam’iyyar a kansu”.
Tsohon gwamnan, wanda ya taka rawa wurin hadakar da ta kai ga kafa jam’iyyar, ya ce an tafka kurakurai ta hanyar sauya sunayen wakilai a zaben fitar da gwanin da aka yi a Ondo.
Ya ce duk da cewa sakamakon bai masa dadi ba, amma ya rungumi kaddara saboda imanin da ya yi da tafarkin demokuradiyya, amma daga baya ta bayyana cewa an tafka magudi.
Wannan shi ne rikici mafi girma da yake fuskantar jam’iyyar ta APC a kasa baki daya tun bayan kafa ta da kuma hawan ta mulki a shekarar 2015.
Masu sharhi za su zuba ido su ga yadda za ta kaya – musamman irin martanin da Shugaba Muhamamdu Buhari ko na kusa da shi za su mayar.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button