Uncategorized

Matashi Mai Aikin Bautar Kasa Ya Kirkiro Wata Manhajar Waya A Najeriya

SADEEQMEDIA — Jaridar Vanguard, ta rawaito cewa wani matashi dake aikin bautar ‘kasa a Minna, mai suna Musa Bello ya kirkiro wata manhajar waya ‘Distress Call Centre’ da zata rika taimakawa mutane ta hanyar wayarwa da mutane kai kan hanyoyi, za kuma a iya amfani da ita wajen kiran neman taimako ko agaji.
A wajen bukin kaddamar da manhajar jiya Laraba a Minna, Bello yace manhajjar zata bayyana taswirar inda mutum yake ta yarda ma’aikatan agaji zasu samu damar isa gareshi ba tare da bata lokaci ba.
Matashin dai wanda yake aikin bautar kasa a gidan Talabijin na NTA, yace wannan aikin wani bangare ne na aikin ci gaban al’umma da yake yi. Ya kara da cwa wannan wata hanya ce da zata baiwa mutane damar neman agajin gaggawa a lokacin da suke bukata. Musamman yayin da akayi hatsarin mota mutane na shan wahala wajen neman ma’aikatan agajin gaggawa, yanzu hakan yazo karshe.
Bello yace manhajjar na dauke da bayanai masu muhimmanci na kare kai da kuma bayanai kan yadda za a iya ceto kananan yara lokacin da suka shiga hatsari, haka kuma manhajar tana da sauki wajen amfani da ita.
Shi dai wannna matashi Bello, ya kammala karatun digirnsa a jami’ar Ahmadu Bello Zariya dake Kaduna.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button