Uncategorized

FATAWAR RABON GADO (55)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (55)
Tanbaya?
Assalamu Alaikum
Akaramakallahu ina neman karin bayani,   Wata mata tarasu, bata da Yaya, ba uwa ba uba, bata da miji, sai wayanda suka hada uwa da uba, da wayanda suka hada uba kawai,, cikin yan uwan nata Akwai maza akwai mata,  a yan ubama akwai maza da mata. Ya gadon ta zai kasan ce ? Allah ya karawa Dr. Lafiya.
Amsa :
Wa alaikumus salam,
Za’a raba abin da ta bari ga yan’uwanta Shakikai, duk namiji ya dau rabon mata biyu. ‘Yan’ uwa da aka hada uba kawai basa GADO matukar akwai namiji a shakikai.
Allah ne mafi sani.
Amsawa Dr Jamilu Zarewa                                     18/Dhul-Hajjah /1437
20/09 /2016
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button