Uncategorized

duвα Wani matashi dan Kaduna ya kirkiro manhaja da za ta ceci rai(hσtunα)

Wani matashi mai hidimar Kasa (Watau NYSC) a Garin Minna, ta Jihar Niger mai suna Musa Bello ya kirkiro wata manhaja da ta za ta sa a rage matsalar da ake samu idan an yi hadarin mota. Musa yayi karatu ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Wannan manhaja ta wayar zamani tana dauke da lambobin ‘yan kwana-kwana da masu bada agaji domin ceton rai yayin da aka samu hadari ko a ina ne a kasar nan.
Wannan manhaja tana dauke da irin wadannan lambobi na neman dauki na Jihohin Kasar nan da dama, sai dai kawai mutum ya zabi Jihar da yake, kana ya nemi lambar da ya ke nema ya latsa

.

Akwai lambobin NEMA; Hukumar da ke bada agaji ta Kasa, akwai kuma lambar neman agajin gaggawa ta Kasar, haka dai kuma akwai lambar ‘Yan kwana-kwana domin hadarin gobara.
Ba nan kadai, ya zama da wannan manhaja mutum na iya aika sako na SMS zuwa wadannan lambobi irin na su Jami’an ‘yan Sanda, da NYSC ta kasa, dsr. Nan gaba ma dai wannan ta’ailiki yace zai kara da lambobi irin na su Hukumar KASTELEA da wasun su.
Wannan manhaja da wannan b nσawan Allah mai suna Musa Bello ya kirkiro zai dauki lambobin kanukawa da sauran masu gyaran motoci a Kasar nan, ko don nan gaba kana tafiya tayar ka ta sace.
Abin dai gwanin sha’awa, duk mai bukatar wannan Manhaj, sai ya garzaya Google Store don ya sauke, kuma kyauta ne ba sai an biya ko taro ba. Idan kuma akwai wasu shawarwari da za a iya badawa, sai a tuntube Malam Musa Bello.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button