Uncategorized

Ba na tsoron duk wani bincike Inji Sarki Sanusi II

JBayan kiran da Babban Lauyan nan watau Femi Falana yayi da a binciki Tsohon babban bankin Kasar nan, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Sarkin ya fito ya bayyana cewa, ba ya tsoron hakan ko kadan, kuma a shirye yake da a nema shi ya amsa tamboyi. Femi Falana SAN ya kira Gwamnati da ta binciki Sarki Sanusi da kuma Charles Soludo game da wasu kudi da ake zargin su karkatar lokacin suna Gwamnan babban Bakin Najeriyar.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyanawa Jaridar Premium Times cewa a shirye yake da a bincike sa, idan bukata ta tashi, zai mika kan sa ga Hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka a Kasar. Sarki Sanusi II ya bayyana cewa a lokacin da yake Gwamnan bankin Najeriya watau CBN, bai taba biyan ‘yan kasuwa kudi da sunan tallafin man fetur ba. Sarki Sanusi II yace hakan bai kuwa taba faruwa ba tare da izinin Gwamnati ba. Gwamnan ya kuma bayyana yadda yayi fada da tallafin man fetur din aka ce ana biyan ‘Yan Kasuwa a wannan lokaci saboda rashin gaskiyar da ta dabaibaye tsarin.
Sarki Sanusi II yace zargin da ake yi, na kwato bankunan Kasar nan da aka yi a lokacin ya ba sa mamaki. Sarki Sanusi yace a lokacin da yake Gwamna sun kwato bankuna ne daga rugujewa, ba kuma ta hanyar mikawa Bankunan kudi ba, sai dai don ka da kudin mutane da ke bankin ya salwanta. Abin da ya faru kuwa shine masu bankunan sun barnatar da kudin Jama’a ko kuma sun bada wawan bashi. Hakan ta sa Bankin na CBN ya dauki wannan mataki, kuma aka kawo AMCON domin bankunan su biya duk kudin da aka ara masu.
Gwamnan bankin Kasar na yanzu, Godwin Emefiele yace laifin Gwamnonin da aka yi a baya ne Kasar ke fama da karancin kudin dala ta Kasar waje
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button