Uncategorized
YIN QUNUTI CIKIN SALLAR ASUBA HAR KULLUM|Sheikh ibrahim jalo jalingo
Ibrahim Jalo Jalingo
YIN QUNUTI CIKIN SALLAR ASUBA HAR KULLUM:
Babu wani abu daga cikin ingantacciyar sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah da yake nuni a kan kebance sallar Asuba koma bayan sauran salloli biyar da ake da su ta hanyar yin Qunuti a cikinta koma bayan sauran sallolin; babu wani hadithi da ya inganta da irin wannan umurni.
**********
Babban hujjar da wadanda suka kebance sallar asuba da Qunuti ke ambata ita ce hadithi na 678 da Imam muslim ya ruwaito daga Sahabi Baraa Bin A’azib cewa:-
((قنت رسول الله صلى الله عليه وسلم في الفجر والمغرب)).
Ma’ana ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti cikin (sallar) Asuba da Magariba)).
Babban abin da zai rusa wannan hanya da su suka dauka ta kafa hujja da wannan hadithi shi ne: kasancewarsu ba su riki yin Qunuti cikin sallar Magariba har kullum ba; ga shi kuwa nassin hadithin ya zo ne a kan sallar Asuba da kuma sallar Magariba gaba daya, a hankalce babu tayadda za a iya rarrabe tsakaninsu cikin hukuncin sai da wani nassi sahihi da zai zo bayan shi wannan hadithin, shi kuwa hakan ba zai samu ba daga gare su.
**************
Gaskiyan al’amari shi ne: Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti a sallar Asuba da sauran salloli na wani dan lokaci saboda yin mugunyar addu’a a kan wasu azzaluman kafurai, kamar yadda ya zo cikin hadithi na 1445 da Abu Dawuda ya ruwaito da isnadi mai kyau, daga Abdullahi Bin Abbas ya ce:-
((قنت رسول الله صلى الله عليه وسلم شهرا متتابعا في الظهر والعصر والمغرب والعشاء وصلاة الصبح في دبر كل صلاة اذا قال: “سمع الله لمن حمده“ من الركعة الاخرة يدعو على احياء من بني سليم على رعل وذكوان وعصية ويومن من خلفه)).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti wata daya a jere cikin “sallar” Azahar, da La’asar, da Magariba, da Isha’i, da sallar Asuba, a karshen ko wace salla in ya ce: “Sami’allahu Liman hamidahu” daga raka’ar karshe yana mugunyar addu’a a kan wasu unguwanni na kabilar Sulaim, da Ri’il, da Zakwan, da Usayyah, mamun da ke bayansa suna cewa amin)).
Kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito cikin hadithi na 677 daga Sahabi Anas Bin Malik ya ce:-
((قنت رسول الله صلى الله عليه وسلم شهرا بعد الركوع في صلاة الصبح يدعو على رعل وذكوان ويقول عصية عصت الله ورسوله)).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi Qunuti na wata guda bayan ruku’i cikin sallar Asuba yana mugunyar addu’a a kan kabilar Ri’il, da Zakwan, yana cewa “kabilar” Usayyah ta saba wa Allah da manzonSa)).
Haka nan Ibnu Majah ya ruwaito hadithi na 1243 da isnadi sahihi daga Anas Bin Malik ya ce:-
((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يقنت في صلاة الصبح يدعو على حي من احياء العرب شهرا ثم ترك)).
Ma’ana: ((Lalle manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance ya yi ta yin Qunuti cikin sallar Asuba yana mugunyar addu’a a kan wata unguwa daga cikin unguwannin Larabawa har na tsawon wata guda sannan ya daina yi)).
***************
Idan wani ya ce: ai karanta Qunuti na dindin cikin sallar Asuba shi ne mazhabar Malikiyyah da Shafi’iyyah, don me za a ce: hakan ba shi ne ya dace da sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ba?!
Sai a ce da shi:
1. Babu wata Mazhaba cikin Mazhabobin da ake da su da take ma’asumiya wacce za a ce babu kure a cikinta ba, babu irin wannan mazhaba har abada.
2. Babu wata Mazhaba cikin Mazhabobin da ake da su da take da matsayin zamantowa Mizani na Shari’ah, a’a Mizanin Shari’ah har kullum shi ne: ingantattun sunnonin Annabi mai tsira da amincin Allah, ko kuma a ce: Alkur’ani da Hadithi…
3. A mazhabar Malikiyyah daura layar da aka rubuta ta da Ayoyin Alkur’ani, ko aka rubuta ta da wasu maganganu masu kyakkyawar ma’ana abu ne da ke halal. To amma duk da yake wannan shi ne Mazhabar Malikiyyah an samu da yawa daga cikin mutanen da suke danganta kawunansu zuwa ga mazhabar Malikiyyar sun zabi barin mazhabar cikin wannan mas’alar sunkoma sun yi riko da abin da umumin sahihin hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah yake nunawa; watau na haramta daura laya ba tare da tafsili ba.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya taimake mu Ya cusa wa al’ummarmu soyayyar manzon Allah da kuma son yin aiki da ingantattun sunnoninsa cikin zukatansu. Ameen.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com