Uncategorized

Gwamnatin Najeriya Na Ranto Makudan Kudi Ta Biya Albashi – Sarki Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Hadeja a Kaduna a Ranar 4 ga Watan Nuwamba, 2015
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II wanda shi ma kwararre ne akan ilimin tattalin azriki yayi tsokaci akan yadda gwamnatin Najeriya ke gudanar da harkokin kasar da manufofinta da yake ganin ba zasu kai kasar koina ba
Sarki Sanusi yace yayi mamakin yadda gwamnatin Najeriya ke ranto makudan kudi tana biyan albashi dasu maimakon ta maida hankalinta gun gina abubuwan da zasu habaka tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummarta.
Yace gina irin su asibitoci da kuma marawa shirye-shiryen inganta ilimi mai inganci su ne zasu kawo cigaba.
Idan gwamnatin dake ci yanzu ta cigaba tana gudanar da harkokinta kamar ta gwamnatin Jonathan, to fa gidan jiya za’a koma, lamarin da ka iya jefa kasar cikin wani mawuyacin hali, inji Sarki Sanusi.
Yakin da gwamnatin Buhari keyi da cin hanci da rashawa zai tabbatar da tattalin arziki mai dorewa. Amma wannan ma ba zai samu ba idan ba’a gina tattalin arzikin da zai rage dogaro ga man fetur ba saboda darajar man fetur din ma tana kushewa a kasuwannin duniya.
Yawancin manufofin gwamnatocin da suka shude akan tattalin arziki sun yiwa kasar illa tare da aiwatar da manufofin da sautari sun sha karo da juna a kasar. Sarkin yace, “tushen matsalolin kasar ke nan”
Sautari wasu da suke ganin su ne suka fi kowa sani su ne kuma zasu iya yin abun a zo a gani, sun cusawa kasar wasu manufofin tattalin arziki da suka karya tattalin arzikin kasar suka kuma kaita suka baro. Abin takaici ne ganin yadda ana ji ana gani aka dinga cigaba da wadannan manufofin.
Najeriya na gaf da durkushewa. Magudi da tallafin da ake ba harkokin sayen kudaden waje sun taimakawa masu hannu da shuni da masu ilimin zamani wajen cin kazamar riba, yayinda karya darajar Nera ya ba wasu damar wawure kudin gwamnati.
Sarki Sanusi yace cigaba da tallafawa nera akan sayen kudin waje ya sa wasu sun zama biloniya dare daya.
Inji Sarki Sanusi, kasashen Afirka da suka dogara ga man fetur sun yi hasara da yawa yayinda tattalin arzikin wadanda basu da man fetur ko kuma sun rage dogaro dashi ya soma habaka kuma suna cikin wadanda habakar tattalin arzikinsu ya fi girma a duniya.
Mulkin mallaka ya cutar da Najeriya saboda yadda aka cigaba da kwashe albarkatunta zuwa turai, bayan an sarafasu a dawo dasu a sayarwa kasar da mugun tsada.
Sarki Sanusi yace “mun haifi namu biloniyoyin tun shekarar 2015 saboda zasu sayi dalar Amurka akan Nera 197 amma sai su sayar da kayansu tamkar sun sayi dala Nera 300 ne. Misali lokacin da babban bankin Najeriya ke sayar da dala Nera 197 mutane na sayenta a kasuwa Nera 300.
Mutum na iya zama cikin gidansa, idan yana da hanya sai ya sayi dala miliyan goma akan Nera 197 kowace dala daya, amma kuma ya sayar da ita Nera 300 kowacce ya ci ribar Nera biliyan daya ba tare da barin gidansa ba.
Irin wannan abun dake faruwa talaka ne yake shan wahala. Shi ne yake biyan masu hannu da shuni, dalili ke nan da suke son gwamnati ta cigaba da tafiya haka, wato a rike masu saniya suna tatsan nono.
Kowa ya san duk kasar da ta bari mutum na cin kazamar riba, kuma yana zaune a gidansa sai yin anfani da tarho kawai ba tare da saka jari koina ba, ya san irin wannan kasar tattalin arzikinta ba zai dore ba, inji Sarki Sanusi.
A karshe Sarki Sanusi yace kowane lokaci babban bankin Najeriya ya sayarwa bankuna dala biliyan daya akan Nera 197 kowace dala daya, jihohi na haarar Nera biliyan dari, kudaden da zasu iya biyan albashi da su, su sa wasu cikin harkokin noma da kiwon lafiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button