Uncategorized

FATAWAR RABON GADO((46) DR JAMILU ZAREWA

           

FATAWAR RABON GADO(46)
Tanbaya :
Salam. Don Allah a taimaka min da amsa wannan Tambayan. Mu shida a gurin mahaifiyar Mu toh Allah yayi wa daya a chikin Mu rasuwa. Mahaifun Mu Allah yayi masa rasuwa Shima. Toh Wadda ta rasu a chikin Mu. Muna da gadonta ko Dai na mahaifiyar Mu ne kawai ?. Kuma muna da Yan uba ko suma suna da gadonta ?. Dun Allah a taimaka min da amsa ko. Nagode.
Amsa :
Wa alaikum assalam
Za’a raba abin da ta bari gida :6, sai a baiwa mahaifiyarku kashi:1, in har akwai namiji a cikin ku sai a baku ragowar kashi biyar din ku raba duk namiji ya dau rabon Mata biyu.
‘yan uba ba sa yin gado mutukar akwai namiji a cikin shakikai.
Allah ne mafi sani :
11/08/2016
Dr Jamilu Zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button