Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (50)|SHEIKH DR.JAMILU JAREWA
FATAWAR RABON GADO (50)
Tamabaya:
Assalamu alaikum. Malamai mutum ne ya rasu ya bar naira 1,900,000. Ya bar matan shi guda biyu, yara maza 7, yara mata 4. Ya rabon gadonsa zai kasance?
Amsa:
Wa alaikum assalam,To dan’uwa kowacce mace daga cikin matansa za’a ba ta 118,750, sai kuma a bawa ‘ya’yansa maza da mata 1662,500 su raba a tsakaninsu, duk namiji zai dau RABON mata biyu.
Allah ne mafi Sani.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com