ZAN IYA BIYAYYA GA MIJINA WAJAN YIN KULUMBOTO
ZAN IYA BIYAYYA GA MIJINA WAJAN YIN KULUMBOTO?
TAMBAYA:
Assalamu alaikum,
Mallam mijina ne ya bani nama in dafa masa amma ko wani yanka akwai alura a jiki sannan da ruwan rubutu na dafa masa. Mallam naji tsoro kuma in banyi ba zai kawo matsala tsakanin mu.
Toh mallam yaya hukuncin wannan abun?
AMSA:
Wa alaikum assalam, ina ba ki shawara ki tambaye shi, In har kin gano sihiri ne aka yi ya halatta ki ki dafawa, ko da kuwa zai sake ki, saboda sihiri kafurci ne. Biyayya ga miji dole ce kamar yadda hadisai da ayoyi suka tabbatar, saidai babu biyayya ga abin halitta wajan sabawa mahalicci, kamar yadda ayoyi a suratul Ankabuti da Lukman suka tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa.
26 Ramadan, 1437H