Uncategorized

MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE?

Advertisment

MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE ?

Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakaatuhu :
Miji ne ya je saduwa da matar sa sai ya kuskure ya saka mata a dubura shin mene ne hukuncinsa?

Amsa:
Wa alaikumus salam wa rahamatullahi wa barakaatuhu, In har da kuskure ya saka mata a dubura, sai ya yi maza ya zare, mutukar ya cire daga zarar ya ji ba wurin ba ne Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba.                                                                        A karshen suratul Bakara “Ya ubangijinmu kar ka ka kamamu in mun manta ko mun yi kuskure” Muslim ya rawaito hadisi cewa: Allah ya zartar da hakan.                                                                                                                                            Ibnu-majah ya rawaito hadisi, Annabi s.a.w. yana cewa: “Allah ya yafewa al’umata abin da suka aikata cikin kuskure”.                                                                                                                        Cigaba da jin dadi a wurin bayan gano kuskuren, yana daga cikin zunubai.                                                     
Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Advertisment

11 Shawwal, 1437 (16/07/2016).

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button