IDAN MAMACI BA SHI DA YA’YA ,ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA
IDAN MAMACI BA SHI DA ‘YA’YA, ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA ?
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Da Allah malam Ina da tambaya kamar haka: shin saurayin da bai yi aure ba, amma yana da iyaye da ‘yan’uwa a raye, zai iya yin wasiyya da rabin dukiyar shi, kasancewar ba shi da ‘ya’ya ? Nagde
Amsa:
A zahirin hadisai ingantattu har wanda ba shi da ‘ya’ya ba zai yi wasici da sama da daya daga cikin uku na dukiyarsa ba, saboda Annabi s.a.w yana cewa da Sahabinsa Sa’ad (RA) lokacin da ya so ya yi wasiyya da mafi yawan dukiyarsa: “Ka bar magadanka cikin wadata, ya fi ka bar su matalauta suna rokon mutane”.
Kasancewar Annabi (S.a.w) ya yi amfani da lafazin magada, hakan sai ya nuna ko ba ‘ya’ya ba za’a yi wasiyya da sama da daya cikin uku na dukiya ba, saboda hakan zai cutar da ragowar magada, ya iya jefa su cikin talauci bayan mutuwar magajinsu.
Aya ta: 12 a cikin suratu Annisa’i tana nuna cewa: Wanda zai mutu ba shi da ‘ya’ya, ba shi da iyaye, ba zai yi wasiyya da abin da zai cuci magadansa ba.
Allah ne mafi sani.
Amsawa: Dr Jamilu zarewa.