IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44,IDDARTA TA CIKA?
IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44, IDDARTA TA CIKA ?:
Tambaya:
السلام عليكم ورحمة الله
Malalm don Allah a taimakamin da amsar wannan tambayar:
Mace ce mijinta ya rasu ya barta da ciki wata daya, bayan sati 2 da rasuwarshi sai cikin yazube to anan ya iddarta take?
1. iddar ta kare?
2. ko zata kirga wata 4 da kwana 10?
in kuma kirgar zat ai daga yaushe zata fara, ranar rasuwarshi ko ranar da cikin ya zube?
na gode.
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Mutukar cikin na ta bai wuce kwana : 44 ba, ba za ta kammala iddar takaba da yin barinsa ba, tun da halittar mutum ba ta fara bayyana ga dan-tayin ba.
Mafi karancin lokacin da halittar mutum take fara bayyana yana farawa ne daga kwana: 80 zuwa 90.
Idan haka ta faru da ita za ta yi idda da wata hudu da kwana goma.
Allah ne mafi sani.d
Dr Jamilu Zarewa. 20/7/2016