Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (35)
Advertisment
FATAWAR RABON GADO (35)
Tanbaya.
Assalamu alaikum warahmatullah. Da fatan Malam yayi Sallah lafiya, Allah ya karbi ibadun mu amin. Malam ina da tambaya akan rabon gado ne: Mace ta rasu ta bar Iyayen ta 2 da kuma mijin ta da ‘ya’ya 7. Maza 4 mata 3 ta bar kuma dukiyar kudi # 200,000 ya rabon gadon zai kasance? Pls Malam na san kana da ayyuka da dama amma a taimaka a amsa min. Allah ya kara fasaha.
Amsa:
Wa’alaykumussalam, za’a raba abin da ta bari gida:12, sai a bawa mijinta kashi :3, a bawa babarta kashi:2, babanta kashi:2, ragowar kashi biyar din sai a bawa ‘ya’yanta su raba, duk namiji zai dau rabon mace biyu.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa :
14/07/2016.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com