BAI HALLATA A CEWA MAI AZUMI BA,YA IBADA!!
BAI HALLATA A CEWA MAI AZUMI BA, YA IBADA ! !
Tambaya:
Salamun Alaikum,
Dr wai wani malami ne yake cewa bai halatta mutum ya cewa dan uwansa musulmi da azumin nan ba ya ibada ba, wai sai dai yace masa ya azumi, Dr. Meye gaskiyar wannan maganar ?.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Azumi ibada ne tun da Allah ya shar’anta shi ne saboda tsoransa, kamar yadda ya fada a suratul Bakara, Ibada ita ce duk abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi na daga zance ko aiki, na fili da na boye kamar yadda malaman musulunci suka bayyana.
Azumi ibada ne tun da Allah ya yarda da shi kuma yana nisanta wanda ya yi shi daga wuta, kuma ya kebance shi da daraja ta musamman wacce babu irinta, kamar yadda hadisai ingantattu suka tabbatar, ga shi kuma sababin shiga aljanna, ibada kuma ita ce hanyar shiga ni’imomin lahira, wannan yake nuna kuskuran waccar maganar da kuma karancin ilimin wanda ya fade ta.
Allah ne mafi sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.