Uncategorized

IZALA TA YABA DA BADA BELIN SHEIKH DR NAZIFI YUNUS JOS

Advertisment

Izala Ta yaba da bada belin Sheikh Dr. Nazeefi Yunus Jos
Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya nuna farin cikin sa ga bada belin da kotu tayi na Sakin Sheikh Dr. Nazeef Yunus, Shugaban yace wannan kadan ne daga cikin irin addu’oin da ‘yan uwa sukayi a lokacin da aka kama shehin Malamin wanda ya shafe kusan shekaru uku a tsare, gashi Allah ya kawo lokacin da zai koma ga iyalansa.
Sheikh Lau ya kara da cewa wannan ya nuna irin adalci da wannan gwamnati ta maigirma shugaban kasar Naijeriya Muhammadu buhari ke da shi wajen maida wa wadanda aka zalunta hakkin su.
Shugaba Bala Lau ya sake kira ga Gwamnatin tarayya da ta sa ke sa ido a gidajen yarin kasar nan, Don rage chunkoso dake chikin gidan, Gwamnati tayi afuwa ga masu zaman jiran Shari’a da ake Ajiye da su fiye da kima.
Shehin Malamin yace Allah (SWT) yanason masu rangwame, saboda haka ma wannan kungiya ta Izala ta kasa, take kai ziyara gidajen yari a fadin kasarnan domin wa’azi, ko a wannan wata ta Ramadan kungiyar ta kai ziyara gidan yari na yola, tayi Wa’azi da gargadi ga ‘yan gidan yari, kuma ta bada tallafin kayan Azumi da sabulai maiyawa ga ‘yan fursuna. Sannan ta biya taara wa mutane 20 daga cikin yan fursuna, wanda aka fiddasu daga chikin gidan yari a matsayin masu ‘yancin komawa ga iyalansu. Wannan duk yana nuna mana muhimmancin lura da yanayin da wadanda suke zaune a gidajen yari suke bukatar a bibiyi lamarin su domin wadanda basu da hakki su koma ga iyalansu suyi rayuwa kamar kowa.
Daga karshe Sheikh Bala Lau ya kara da addu’ar Allah ya kare duk wani musulmi daga shiga irin wannan jarrabawar, yasa mu gama da duniya lafiya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button